The Body as a Toolbox in the Hausa Language

Autor/innen

  • Aliyu Yalubu Yusuf

DOI:

https://doi.org/10.18716/ojs/aaeo/2021_3479

Abstract

Tsokaci Wannan makala ta tattauna batu ne na karin magana masu dangantaka da sassan jikin Dan Adam da kuma aiyukan sassan jiki a harshen Hausa. A wasu lokutan, Hausawa kan yi amfani da karin magana masu dangantaka da sassan jikin Dan Adam a wani irin salo da kai kace wadannan Karin maganganun wasu kayan aiki ne da ake aikata aiki da su a gaske ko kuma a tinani. Don haka wannan makala ta yi kokarin zakulo wadannan karin maganganun sannan kuma ta fayyace su ta hanyar mahangar “Linguistic Relativity’ wanda Benjamin Lee Whorf ya samar. Ta hanyar amfani da ‘purposive sampling’, wannan makala ta zakulo wadannan karin maganganu a cikin wasu litattafai na karin magana da kuma sauraron hirarraki a tsakanin al’umar Hausawa dake garin Kano a Nijeriya. Bayan kallo na tsanaki tare da fayyace wadannan karin maganganu, wannan makala ta gano cewa Hausawa su na yawan amfani da karin maganganu masu dangantaka da sassan jikin Dan Adam ta hanyar da mutum zai yi tsammanin cewa wadannan karin maganganu wasu kayan aiki ne da ake sarrafa su a yi aiyuka. Wannan watakila yana faruwa kasancewar yadda yanzu haka a kasashen Turai yawanci injina ne suke yin aiyukan da a da mutune ne ke yi da jikinsu kamar irin su dako da daka da tafiye-tafiye da sauransu. Mu kuwa a nan kasashen Afirka har yanzu mutune da kan su ke yin yawancin irin wadannan aiyuka. Hakan shi ya sa watakila har yanzu wadannan karin maganganu su ke da matukar amfani a rayuwar al’umar Hausawa.

Downloads

Veröffentlicht

2021-10-16

Ausgabe

Rubrik

Proceedings

Zitationsvorschlag

Yusuf, A. Y. (2021). The Body as a Toolbox in the Hausa Language. AAeO - Afrikanistik-Aegyptologie-Online. https://doi.org/10.18716/ojs/aaeo/2021_3479